Ousmane Dembele ya zura kwallaye uku mafi sauri na biyu a tarihin gasar Kofin Duniya yayin da Faransa ta doke Norway 4-1 don tabbatar da cewa ta zo ta ɗaya a Rukuni na I.
Wasan mai ƙayatarwa da aka buga a filin wasa na Boston, ya cika burin da aka yi kafin wasan, kodayake Norway ta ba da mamaki da ta canza ’yan wasa 10 daga cikin wadanda suke fara buga mata wasa, ciki har da barin Erling Haaland a kan benci har ƙarshen wasan.
Dembele ya zura ƙwallaye ukun kafin minti na 32 da fara wasa, yayin da Thelo Aasgaard ya ci wa Norway kwallo ɗaya.
-
Gasar Cin Kofin Duniya 2026: Turkiyya ta doke Amurka 3-2
-
Ƙungiyar da za ta lashe gasar NPFL mai zuwa za ta karɓi kyautar kuɗi naira biiyan 1
Burin Norway na dawowa Ƙungiyar da za ta lashe gasar NPFL mai zuwa za ta karɓi kyautar kuɗi naira biiyan 1 cikin wasan ya zo karshe bayan da Jorgen Strand Larsen ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron raga, yayin da nasarar da Faransa ta samu ya tabbata ne bayan da aka cire jarumin wasan Dembele a minti na 65, sannan Desire Doue ya rufe kofa da ƙwallo ana dab da tashi a wasan.
Kyalian Mbappe ne ya taimaka wa Dembele zura ƙwallaye biyu.
Duk da rashin sa’ar Mbappe na zura ƙwallo a wasan, a yanzu shi da Dembele suna da ƙwallaye huɗu kowanne a gasar, wanda ya sa Faransa ta zama ƙasa ta farko a gasar Kofin Duniya tun bayan Poland a 1974 da ke da ’yan wasa biyu da suka zura ƙwallaye haka a matakin rukuni.