Hukumar dakile cutuka masu saurin yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce tana matsa ƙaimin daƙile shigowar cutar Ebola cikin ƙasar.

Babban Daraktan hukumar Dakta Olajide Idris ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya ce hukumar na ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da na shige da fice, domin matsanta bincike akan iyakoki.

Ya ce matafiya masu shigowa ƙasar za su ci gaba da cike takardun bayanan lafiyar su, domin bibiyar mutanen da kan kasance haɗari.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta amince da kashe Naira miliyan 785.3 domin shirye-shiryen daƙile shigowar cutar, ƙarƙashin shirin ko-ta-kwana a matakin jihohi.

Sai dai ya ce yawancin cibiyoyin killace marasa lafiya da ɗakunan gwaje-gwajen da aka kafa lokacin annobar COVID-19 sun lalace saboda rashin kulawa, yayin da wasu ke fama da matsalar wutar lantarki.

Game da cutar kwalara, Dakta Olajide Idris ya ce adadin mace-mace ya ragu a mafi yawan jihohi, in banda jihar Borno da matsalolin ruwa da tsaftar muhalli suka ƙara ta’azzara lamarin.

Ya buƙaci gwamnatocin jihohi su ƙara zuba jari a shirye-shiryen rigakafi da dakile barkewar cututtuka domin gujewa yaɗuwar su zuwa sassa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *