Hedikwatar Sojojin Najeriya ta sauya wa wasu manyan hafsoshi wuraren aiki, a wani mataki na ƙara inganta aiki da kuma ƙarfafa tsaron ƙasa.

Babban Hafsan Sojojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ne ya amince da wannan sauyin wanda ya shafi kwamandojin rundunoni, shugabannin cibiyoyin horo, da kuma manyan jami’an ma’aikata a Hedikwatar Soji.

A wata sanarwa da Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar Kanar Appolonia Anele, ya bayyana cewa Manjo Janar WM Dangana ya zama sabon  mai kula da Runduna ta 3 ta Sojojin Najeriya kuma Kwamandan Haɗin Gwiwar Operation ENDURING PEACE, inda ya maye gurbin Manjo Janar EF Oyinlola.

Haka kuma, Manjo Janar EI Okoro ya karɓi ragamar Runduna ta 6 ta Sojojin Najeriya tare da zama Kwamandan Bangaren Ƙasa na Operation DELTA SAFE, bayan maye gurbin Manjo Janar EE Emeka.

A ɓangaren sauran muƙamai, Manjo Janar JR Lar ya zama Kwamandan Hedikwatar Barikin Sojoji, yayin da Birgediya Janar OM Oyekola ya zama Muƙaddashin Sakatare na Soji (Army), Birgediya Janar I Waziri kuma ya ci gaba da zama Shugaban Ma’aikata a ofishin CO.

Haka zalika, Birgediya Janar IB Buhari ya zama Kwamandan Hedikwatar Birgediya ta 63, yayin da Birgediya Janar K Rabiu ya karɓi ragamar Birgediya ta 31 ta Makamai.

Yayin da Manjo Janar O Adegbe ya zama Daraktan Leken Asiri da Tsaro a Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa.

A fannin horar da soja, Manjo Janar KE Chigbu ya zama Mataimakin Shugaban Kwalejin Tsaro ta Ƙasa, yayin da Manjo Janar SD Makolo ya zama Kwamandan Makarantar Tankokin Soja.

Birgediya Janar U Ahmad ya zama Kwamandan Depot na Sojoji da ke Zariya

Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Manjo Janar KO Ukandu a matsayin Manajan Darakta na Kamfanin Gidajen Sojoji (PHDL), da Manjo Janar AI Allison a matsayin Manajan Darakta na Kamfanin Defence Properties Limited.

Babban Hafsan Sojojin Ƙasa ya umarci sabbin shugabannin da su nuna ƙwarewa da jajircewa da nagarta wajen gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da kare martabar Najeriya da tsaron al’umma.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *