Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa an kama wasu kwamandojin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP guda bakwai a Filin Jirgin Sama na Katsina yayin da suke dawowa daga aikin Hajji a ƙasar Saudiyya.
Ya ce an samu nasarar kamen ne sakamakon haɗa bayanan Hukumar Bayar da Lambar Shaidar Dan Ƙasa (NIMC) da na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya da kuma tsarin bayanan hukumomin tsaro na ƙasa da ƙasa.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a bayan Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan Dokar Hukumar Bayar da Lambar Shaidar Ƙasa (NIMC) ta shekarar 2026.
- DSS ta saki mutumin da aka tsare bisa zargin Boko Haram, ta ba shi tallafin Naira miliyan uku
- Ƙudirin kafa ’yan sandan jihohi na ƙara samun goyon baya a Nijeriya
Gwamnatin Tarayya ta ce sabuwar dokar za ta ƙarfafa tsarin tantance bayanan ‘yan ƙasa, inganta tsaron ƙasa, sauƙaƙa samar da ayyukan gwamnati da kuma hanzarta sauyin fasahar zamani.
A cewar Tunji-Ojo, sabuwar dokar za ta ƙara inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, ta ƙarfafa sahihancin tsarin Lambar Shaidar Ƙasa (NIN), tare da taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, satar bayanan jama’a, laifukan kuɗi da sauran barazanar tsaro.
Ya ce haɗa bayanan NIMC da sauran bayanan gwamnati ya riga ya fara haifar da sakamako mai kyau, inda ya bayyana cewa kwamandojin Boko Haram da ISWAP bakwai da aka kama a makon da ya gabata an miƙa su ga Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS domin ci gaba da bincike.
Ministan ya ƙara da cewa kafin aiwatar da waɗannan sauye-sauye, hukumomin gwamnati na gudanar da tsarin tantance bayanai daban-daban ba tare da haɗin kai ba. Ya ce a halin yanzu ba za a iya samun fasfo na Nijeriya ba sai an tabbatar da bayanan mutum ta hanyar tsarin NIMC, matakin da ya ce zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da inganta sahihancin bayanan ‘yan ƙasa.