George Akume Sakataren Gwamnatin Tarayya

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya yi Allah-wadai da kisan Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na Jihar Benue, Alhaji Ardo Risku, tare da wani abokinsa, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban hari kan ƙoƙarin samar da zaman lafiya da sulhu da ake yi a jihar.

Shafin Muryar Najeriya ya ruwaito cewa Sanata Akume ya ce bai kamata miyagun mutane su samu damar rusa cigaban da aka samu wajen dawo da tsaro da zaman lafiya tsakanin al’ummomin Jihar Benue ba.

Ya yi kira ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa an kamo waɗanda suka aikata wannan kisa domin su fuskanci hukunci.

Yayin da yake miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da kuma shugabannin ƙungiyar MACBAN, Sanata Akume ya buƙaci mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa binciken da ake gudanarwa

Hakazalika, ya ƙarfafa al’umma da su ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin samar da zaman lafiya, yana mai sake jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na magance matsalar rashin tsaro a sassan ƙasar baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *