Sojojin Operation WHIRL STROKE, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron al’umma na Jihar Benue, sun daƙile wani hari da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai a Kasuwar Doya ta Tor Donga da ke Jihar Benue.
Hakan na ƙunshene cikin wata sanarwa da muƙaddashin kakakin rundunar Ahmad Zubairu Zubairu ya fitar.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 28/6/2026 yayin da sojojin ke gudanar da sintirin yaƙi da kuma ayyukan ƙarfafa gwiwar al’umma.
- Sojoji sun hallaka Lakurawa biyu a Jihar Kebbi
- ’Yan sanda sun kama wasu ’yan’uwa biyu kan zargin yi wa ƙaramar yarinya fyade
- Baiwa ƙananan ƴan kasuwa jari ke ɓunƙasa tattalin arziƙi-Mohammed Idris
A yayin musayar wuta da ‘yan ta’addan, an kashe mutum biyu daga cikinsu masu suna Dantaraba da Golozo.
Bayan kammala samamen, sojojin sun ƙwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, kwanson alburusan AK-47 guda ɗaya, bindigar hannu guda ɗaya da ta lalace, kwanson alburusan bindigar hannu guda ɗaya, harsasai shida na 7.62 mm NATO, harsasai tara na bindigar hannu mai nauyin mita 9, katin ATM guda ɗaya, katin ATM na Moniepoint guda ɗaya, da sauran kayayyaki.
Sanarwar ta ce wannan nasarar ta tabbatar da ci gaba da tsaron ‘yan kasuwa da mazauna yankin, tare da ba su damar gudanar da harkokinsu ba tare da fargabar hare-haren ‘yan ta’adda ba.
Da yake yabawa dakarun, Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation WHIRL STROKE, Manjo Janar Moses Gara, ya ce ƙwarewa, jajircewa da saurin daukar matakin da suka nuna sun taimaka wajen hana aukuwar mummunan hari da ka iya jawo asarar rayukan fararen hula da kuma kawo cikas ga harkokin kasuwanci.
Ya kuma yabawa jami’an tsaron alumma na Jihar Benue bisa gudummawar da suke bayarwa wajen yaƙi da miyagun laifuka a jihar.
Hakazalika, Manjo Janar Gara ya gode wa al’umma bisa ci gaba da bayar da sahihan bayanan sirri ga hukumomin tsaro, yana mai jaddada cewa haɗin kan jama’a da jami’an tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.