Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa za a gudanar da wata ganawa tsakanin jami’an Amurka da Iran a ranar Talata a birnin Doha na ƙasar Qatar, bayan da ya ce Iran ta nemi a sake komawa teburin tattaunawa bayan musayar hare-hare da suka yi barazanar rusa yarjejeniyar wucin gadi da ke tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai wani babban jami’in gwamnatin Iran ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa babu wata ganawa da aka tsara tsakanin jami’an Iran da na Amurka, ko ma ƙungiyoyin ƙwararru (technical teams), a Doha a wannan makon.

A gefe guda kuma, Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya sanar da cewa za a saki dala biliyan 6 daga cikin dala biliyan 12 na kuɗaɗen Iran da aka daskarar, waɗanda ke hannun gwamnatin Qatar, domin mayar da su ƙasar.

Mai sharhi kan harkokin siyasa, Abbas Aslani, ya ce duk da cewa sauran sassan tattaunawar tsakanin Iran da Amurka sun tsaya cik, batun bai wa Iran damar amfani da dala biliyan 6 da aka daskarar na samun ci gaba.

Ya bayyana cewa wannan na daga cikin yarjejeniyar da Qatar ta taimaka wajen sasanta tsakanin Iran da Amurka.

Ya tuna cewa a shekarar 2023, a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Amurka Joe Biden, an cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu domin sakin dala biliyan 6 na kadarorin Iran da aka daskarar a Koriya ta Kudu.

Daga baya aka mayar da kuɗin zuwa Qatar a matsayin mai shiga tsakani, da fatan Iran za ta samu damar amfani da su.

A halin da ake ciki, dakarun Isra’ila sun kashe wasu Falasdinawa uku a Zirin Gaza, ciki har da wani yaro, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta taimaka wajen samarwa.

Hare-haren na ci gaba ne yayin da ake ci gaba da zargin Isra’ila da aikata manyan laifuffuka kan fararen hula a Gaza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *