A daidai lokacin da tattalin arziƙin Najeriya ke fuskantar ƙalubale mafi tsanani, wani tsohon bidiyon tattaunawa tsakanin shahararren ɗan jarida Seun Okinbaloye da Zainab Buba Galadima ya sake ƙarfafa gwiwar masu fashin baƙi a kan cewa “an faɗa mana amma mun ƙi ji.”
Watanni tara ke nan tun bayan da Zainab Buba Galadima, wacce aka sani da faɗin gaskiya ba tare da tsoro ba, ta yi wani babban gargaɗi game da abin da ta kira “Guguwar da ke tafe”.
A yau, kalaman nata sun zama tamkar madubi ga halin da ƙasar nan ke ciki.
A hirar, Zainab ba wai kawai adawar siyasa ta yi ba, ta yi bayani ne kan matsalolin da suka shafi tushen rayuwar talaka.
Ta buga misali da mabarata da ta ce sun daina yin barar cikin girmamawa zuwa ƙwanƙwasa gilashin mota da ƙarfin tsiya mai kama da ƙwace.
Ta nanata cewa idan wutar talauci da rashin tsaro ta ruru a arewacin Najeriya to babu inda zai tsira a faɗin ƙasar nan.
Zainab ta fito ƙarara tana sukar masu faɗa-a-ji, waɗanda ta ce suna ƙoƙarin nuna cewa komai yana tafiya daidai, alhalin talakan ƙasa yana kukan yunwa.
“Ina tsoron guguwar da ke tafe… idan Arewa ta ruguje, to Najeriya baki ɗaya ta tafi”, inji ta.
Faifan bidiyon nata ya bayyana tsoron da take da shi kan makomar ƙasar nan tun bayan zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa da aka yi a shekarar da ta gabata, tana mai cewar wannan ba kyakkyawan yanayi ba ne da zai sanya masu mulki su yi barci.
Tun a wancan lokaci gwamnati ta ce tana iyakacin ƙoƙarin sauke haƙƙin al’umma, sai dai ‘ƴan adawa suna zargin tana yunƙurin mayar da ƙasar kan tsarin mulkin jam’iyya guda.
Shin kuna ganin gwamnati tana daukar matakan da suka dace ko kuwa akwai sauran aiki?