Wani sabon binciken ra’ayin jama’a da kamfanin Ipsos ya gudanar wa Reuters ya nuna cewa goyon bayan Amurkawa ga yaƙin da ake yi da Iran ya ragu zuwa mafi ƙanƙantar mataki tun farkon rikicin, inda mutum ɗaya kacal cikin uku ke nuna goyon baya .

Binciken ya nuna cewa kashi 69% na Amurkawa na ganin Shugaba Donald Trump bai yi cikakken bayani kan dalilan shigar sojojin Amurka cikin rikicin Iran ba.

Wannan ra’ayi ya haɗa har da kusan mutum huɗu cikin goma daga jam’iyyar Republican.

Sai dai duk da haka, ƙimar amincewar jama’a da yadda Trump ke gudanar da mulki ta ƙaru zuwa kashi 37%, wato maki uku sama da yadda take a watan da ya gabata.

Tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare a ranar 28 ga Fabrairu, goyon bayan yaƙin bai taɓa kaiwa kashi 40% ba.

Wannan ya bambanta da irin goyon bayan da yaƙin Iraki da na Afghanistan suka samu a farkon shekarunsu, inda mafi yawan Amurkawa suka mara musu baya.

Sai dai Shugaba Trump ya sha bayyana manufofi daban-daban game da yaƙin, ciki har da hana Iran mallakar makamin nukiliya da rage ƙarfin makamai masu linzami na ƙasar da kuma taimaka wa Iraniyawa wajen sauya shugabancinsu.

Sai dai Fadar White House ta ce shugaban ba zai yanke shawara bisa sakamakon binciken ra’ayin jama’a ba, tana mai jaddada cewa gwamnatin za ta ci gaba da kokarin hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Wasu daga cikin waɗanda aka tattauna da su sun bayyana rashin gamsuwarsu da rikicin.

Alex Womack, wani ɗan jam’iyyar Republican daga jihar Georgia, ya ce:

“Ba a bayyana mana dalilin da ya sa muka fara wannan yaƙi ba. Ban san dalilin ba.”

Shi ma Rhyan Anderson, wanda ya zaɓi Trump a zaɓen 2024, ya ce ya kamata shugaban ya fi mayar da hankali kan matsalolin cikin gida maimakon shiga rikice-rikicen ƙasashen waje.

Wasu daga cikin manyan dalilan da yasa Amurkawan suka ƙi goyawa Trump baya sun haɗa da:

Rashin bayyana manufar yaƙin a fili:

Kashi 69% na waɗanda aka yi wa tambayoyi sun ce Trump bai bayyana a sarari dalilin da ya sa Amurka ta shiga yaƙin Iran da kuma abin da take son cimmawa ba.

Sauya manufofin yaƙin akai-akai:

Trump ya bayyana dalilai daban-daban game da yaƙin, ciki har da taimaka wa Iraniyawa su sauke shugabanninsu, lalata ƙarfin makamai masu linzami na Iran, da kuma hana Iran mallakar makamin nukiliya. Wannan sauya bayanai ya sa mutane da yawa suka rikice

Buƙatar a fi mayar da hankali kan matsalolin cikin gida:

Wasu Amurkawa na ganin ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen magance matsalolin da ke cikin ƙasar, maimakon shiga yaƙe-yaƙe a ƙasashen waje ko taimaka wa ƙawayen Amurka

Fargabar shiga dogon yaƙi:

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Trump ya yi alkawarin cewa ba zai jefa Amurka cikin dogayen yaƙe-yaƙe ba. Wasu masu sukar gwamnati na ganin shigar Amurka cikin wannan rikici ya saɓa wa wannan alƙawari, kuma suna tsoron yaƙin zai ɗauki lokaci mai tsawo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *