Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa Amurka ba ta da wata rawa a tattaunawar da Iran da Oman suka yi kwanan nan kan yadda za a gudanar da harkokin mashigin ruwa na Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga zirga-zirgar jiragen ruwa a duniya.
Yayin taron manema labarai na mako-mako Mai magana da yawun ma’aikatar, Esmaeil Baqaei, ya ce “Waɗannan tattaunawar ba su da wata alaƙa da Amurka.
Ya ce: “Batu ne tsakanin Iran da Oman kawai, kuma tattaunawar na ci gaba.”
Ya kuma ƙara da cewa mashigin Hormuz “har yanzu a rufe take.”
- MDD ta ayyana shekarun 2027 zuwa 2036 a matsayin shekarun ƙarfafa zaman lafiya a duniya
- Lauyoyi sun buƙaci a saki tsohon Shugaban Nijar bayan cika shekaru uku da juyin mulki
- Guterres ya yi kira ga Duniya ta taimaka wa Siriya bayan yaƙin basasa
Mataimakan ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu sun gudanar da tattaunawa a ranakun Juma’a da Asabar kan “ƙa’idoji na bai ɗaya da kuma hanyoyin aiki” domin tabbatar da amintacciyar zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin.
Zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz, wanda yake ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufurin kaya da makamashi a duniya, na ƙarƙashin ikon Iran tun bayan barkewar yaƙi tsakaninta da Isra’ila da Amurka a ranar 28 ga Fabrairu.
A cikin kwanakin baya, dakarun Revolutionary Guards na Iran sun dakatar da wasu jiragen ruwa da dama, ciki har da guda shida a safiyar ranar Litinin, waɗanda suka yi ƙoƙarin wucewa ta mashigin ta wata hanya da ba ta cikin hanyar da gwamnatin Iran ta amince da ita.
Iran ta jaddada cewa tana son ci gaba da riƙe ikon gudanar da mashigin, ciki har da karɓar kuɗaɗen hidimar da ake biya, tare da ci gaba da bai wa Oman damar taka rawa a matsayin ƙasar da ke bakin mashigin.
Rushewar yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka da aka sanya wa hannu a watan Yuni ya haifar da kwanaki 13 na musayar hare-hare tsakanin ɓangarorin biyu, kodayake an dakatar da faɗan tun daga safiyar ranar Asabar.
A ranar Litinin, Esmaeil Baqaei ya soki Amurka, yana mai cewa halayenta a cikin ’yan shekarun nan “sun yi kama da na ƙungiyar ’yan daba (mafia) wacce ba ta bin wata doka ko ƙa’ida.”