Wasu majiyoyin soji sun bayyana a ranar Litinin cewa sojojin Sudan sun sake ƙwace iko da wani muhimmin babban titi da ke haɗa babban birnin ƙasar, Khartoum, da birnin El-Obeid

Wannan na zuwa ne bayan dakarun Rapid Support Forces (RSF), waɗanda ke yaƙi da gwamnatin Sudan, sun shafe watanni suna tara mayaƙa a kewayen birnin El-Obeid

Rahotanni sun ce yanzu an kori dakarun RSF zuwa yammacin yankin, inda aka tilasta musu janyewa daga kan wannan babban titin.

Birnin El-Obeid na da matuƙar muhimmanci sakamakon kasancewar sa kan mahadar manyan hanyoyi.

Babban titin da ya nufi arewa da kudu yana haɗa birnin da Khartoum, yayin da hanyar gabas da yamma ke haɗa yankunan Darfur, inda RSF ke da ƙarfi, da yankunan tsakiyar ƙasar da gabashinta da ke ƙarƙashin ikon sojojin gwamnati.

Ko da yake har yanzu ba a buɗe babban titin zuwa Khartoum ga fararen hula ba, wani jami’in soji ya ce ci gaban da sojojin suka samu ya buɗe wata sabuwar hanyar kai kayayyakin agaji da kayan masarufi zuwa birnin El-Obeid.

Rikicin tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF ya ɓarke ne a watan Afrilun shekarar 2023.

A cewar ma’aikatan agaji, rikicin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 200,000.

Haka kuma, rikicin ya haifar da mummunar matsalar yunwa mafi girma a duniya, inda miliyoyin mutane ke fuskantar ƙarancin abinci da buƙatar agajin jin ƙai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *