Jirgin na biyu da gwamnatin tarayya ta aika domin kwaso ‘yan Nijeriya daga Afirka ta Kudu ya isa Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, dauke da mutane 269.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta bayyana cewa jirgin na kamfanin Air Peace ya sauka a safiyar Talata, 30 ga Yuni, 2026, da misalin ƙarfe 10:48 na safe.

Wannan na zuwa ne bayan dawowar wasu ‘yan Nijeriya 66 a ranar 24 ga Yuni ta jirgin South African Airways, sakamakon tallafin da wani ɗan Nijeriya ya bayar domin sauƙaƙe jigilar su zuwa gida.

Jami’an Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Afirka ta Kudu ne suka raka mutanen da suka dawo, yayin da manyan jami’an Ma’aikatar Harkokin Waje, ƙarƙashin jagorancin Daraktan Sashen Harkokin Afirka, Ambasada Haruna Ali-Gombe, suka tarbe su a hukumance a filin jirgin saman.

Yayin tarbar waɗanda suka dawo, Ambasada Ali-Gombe ya tabbatar musu cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da muradun ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje.

Ma’aikatar ta ce duk da wa’adin ranar 30 ga Yuni da gwamnatin Afirka ta Kudu ta gindaya wa baƙin haure marasa cikakkun takardu su fice daga ƙasar, shirin dawo da ‘yan Nijeriya na ci gaba da gudana.

A cewar ma’aikatar, ana sa ran ƙarin jiragen za su iso Nijeriya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa domin dawo da sauran ‘yan ƙasar da aka tantance kuma suka amince su koma gida da son ransu.

Gwamnatin Tarayya ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin Afirka ta Kudu domin tabbatar da kariya da walwalar ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *