Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Prince Adeniyi Adeyemi Matthew ba jami’in gwamnatin tarayya ba ne, kuma hukumar da yake ikirarin jagoranta babu ita a tarihi.

Sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar ta ce an gurfanar da Adeyemi da wasu mutum biyu kan zargin jabun takardu, kwaikwayon jami’in gwamnati da damfara.

Gwamnatin ta ce binciken ‘yan sanda ya gano cewa Adeyemi ya yi amfani da takardun bogi wajen gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar.

Rahoton binciken ya kuma ce an gano asusun bankuna da takardu da ake zargin an buɗe da sunayen hukumomin bogi.

A cewar gwamnatin, an fara binciken lamarin ne tun Oktoban 2025 bayan Ofishin Babban Hafsan Ma’aikatan Shugaban Ƙasa ya kai ƙorafi ga jami’an tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran za a ci gaba da shari’ar Adeyemi a ranar 27 ga Yulin 2026.

A ƙarshe, Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci jama’a su jira hukuncin kotu maimakon yanke hukunci tun kafin a kammala shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *