Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin gyaran hanyar Bama zuwa Banki da kuma hanyar Dikwa–Gamboru–Ngala a Jihar Borno, inda ta bayyana ayyukan a matsayin muhimman jarin da za su sake buɗe hanyoyin kasuwanci masu muhimmanci da ƙarfafa ayyukan tsaro da kuma hanzarta farfaɗowar tattalin arziki a yankin Arewa maso Gabas bayan tashe-tashen hankulan da suka addabi yankin.
Da yake ƙaddamar da aikin a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce waɗannan ayyuka na nuna ƙudirin gwamnatin Tinubu na dawo da zirga-zirga da farfaɗo da amincewar jama’a ga tsaro da kuma sake haɗa al’ummomin da suka fuskanci ɓarna sakamakon shekaru na ta’addanci da rashin kula da ababen more rayuwa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa yankin da ake gudanar da aikin yana Arewa maso Gabashin Najeriya kuma yana iyaka da ƙasar Kamaru.
Hanyar Bama–Banki mai tsawon kilomita 49.15 hanya ce mai layi biyu wadda ta tashi daga garin Bama zuwa kan iyakar Najeriya da Kamaru.
- Oluremi Tinubu ta bai wa ɗakunan karatu na makaranatun Gwamnati littattafai 140, 000
- Gwamati ta san da labarin hukumar bogi-Mataimakin Shugaban ƙasa na musammam
- Jami’ar jin ƙai ta raba rigunan tsaron ruwa ga masu ceton rayuka a Kogin Kaduna
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar, Shettima ya ce ingantattun hanyoyi na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Ya ƙara da cewa lalacewar hanyoyi na jawo asara mai yawa ga ‘yan kasuwa da iyalai da al’ummomi.
Tun da farko, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ababen more rayuwa su ne tubalin ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Ya ce kammala waɗannan hanyoyi zai ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar Borno tare da ƙarfafa cinikayya da ƙasashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar.
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa an fara ba da kwangilar ayyukan hanyoyin biyu ne tun a shekarar 2021 kan kuɗi sama da Naira biliyan 55.
Sai dai yanzu kuɗi gyaran hanyar Bama–Banki ya haura Naira biliyan 70, yayin da mataki na farko na gyaran hanyar Dikwa–Gamboru ya kai Naira biliyan 67.