A yanzu Kylian Mbappe na da kwallaye 19 cikin wasanni 19 da ya buga na Gasar Cin Kofin Duniya bayan ya zura bugun fenareti a minti na 70, wanda ya taimaka wa Faransa ta kai matakin kwata fainal da ci 1-0 a kan Paraguay.
Wasan, wanda suka buga a filin wasa na Philadelphia ranar Asabar ya kasance mai zafi har ma da samun tashin hankali sau da yawa, yayinda Mbappe ya tsinci kansa cikin matsin lamba amma ya kwantar da hankalinsa don tabbatar da ci gaban tawagarsa.
-
Moroko ta cire mai masaukin baƙi Canada daga gasar Cin Kofin Duniya
-
Wikki Tourists FC ta bayyana Bala Abubakar Mohammed a matsayin sabon kociyanta
Sai dai a wasan gaba Faransa za ta haɗu ne da Moroko a matakin gaba na kwata fainal. Sun taɓa haɗuwa shekaru huɗu baya a Qatar 2022, inda Faransa ta doke Atlas Lions da ci 2-0 a wasan kusa da na ƙarshe.
Mbappe ya ci gaba da ƙalubalantar Lionel Messi kan wanda zai lashe kyautar takalmin Zinare inda kowannensu na da kwallo 7 a wannan gasa.