Sautin murya da ya bazu a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin na ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar ADC Alhaji Isa Ashiru ne, ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar da kuma tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
A cikin sautin da ake ta yaɗawa, an ji wanda ke magana yana sukar Malam El-Rufai tare da cewa shiga jam’iyyar ADC wata dabara ce ta siyasa domin samun tikitin takarar gwamna.
Haka kuma an yi zargin cewa ya bayyana dangantakarsa da El-Rufai a matsayin ta anfani na siyasa kawai, ba wai saboda goyon baya na gaskiya ba.
Sai dai wata majiya daga cikin manyan jiga-jigan ADC a Kaduna ta Arewa, wadda ta nemi a sakaya sunan ta saboda ba ta da izinin yin magana a madadin jam’iyyar, ta musanta sahihancin sautin.
Majiyar ta ce, a wannan zamani na fasahar ƙirƙirar sauti ta hanyar basirar na’ura (AI), ana iya ƙirƙirar irin waɗannan sauti domin bata sunan mutane, inda ta zargi abokan hamayyar siyasa da ƙoƙarin ɓata sunan Isa Ashiru kafin zaɓe.
A gefe guda kuma, wata majiya ta bayyana cewa magoya bayan Malam El-Rufai sun gudanar da wani taro domin tattauna batun, inda suka jaddada cewa suna nan daram wajen ci gaba da mara masa baya da kuma kare mutuncinsa a jihar Kaduna
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Alhaji Isa Ashiru bai fitar da wata sanarwa a hukumance kan batun ba. Ƙoƙarin jin ta bakinsa ta wayar tarho da kuma saƙonnin WhatsApp bai yi nasara ba.
Isa Ashiru ya taɓa fafatawa da Malam Nasir El-Rufai a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2015 amma ya sha kaye, kafin daga bisani ya koma PDP, inda ya samu tikitin takarar gwamna sau uku, amma ya sha kaye a zaɓukan 2015, 2019 da 2023.
Yanzu kuma ya koma jam’iyyar ADC, inda ya sake samun tikitin takarar gwamna.
