Kocin Super Falcons, Justine Madugu ya zaɓi tawagar ‘yan wasa 25, ciki har da Kyaftin Rasheedat Ajibade, da mai tsaron raga Chiamaka Nnadozie, da kuma ‘yar wasan gaba Asisat Oshoala, domin kare kambun Gasar Cin Kofin Mata na Afirka da Najeriya ta lashe a wancan karon.
Gasar na karo na 14 wanda za a gudanar a Moroko, za a fara shi ne daga ranar 26 ga Yuli zuwa 16 ga Agusta 2026.
Najeriya, wadda ke riƙe da kambun, na neman sake lashe kofin a karo na 11 domin sake ajiye wani babban tarihi, ta na cikin Rukuni na C tare da Masar da Zambia da Malawi, masu halartar gasar a karon farko.
Dukkanin ƙasashe huɗu da suka kai wasan kusa da na ƙarshe na gasar, wadda ƙasashe 16 za su fafata a karon farko, za su samu tikitin kai tsaye zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata na shekara mai zuwa a Brazil.
-
Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Cin Kofin Ƙwallon Raga ta Rairayi ta Afirka ta 2027
-
Flamingos sun isa Lomé don fafatawar ƙarshe da Benin a wasan nemar tikin shiga Gasar Duniya
-
City ta sayi mai tsaron raga Charles
Super Falcons, wadda ke halartar Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata tun daga karo na farko da aka fara a China shekaru 35 da suka gabata, ta doke masu ɗaukar nauyin gasar Atlas Lionesses na Moroko da ci 3-2 a wasan ƙarshe domin lashe kofin nahiyar na 10 a tarihi.
Cikin ‘yan wasa 25 da aka gayyata domin fafata Gasar ta WAFCON na karo na 14, akwai masu tsaron raga da ska haɗa da Chiamaka Nnadozie (Brighton Hove & Albion, Ingila); da Comfort Erhabor (Portsmouth Ladies, Ingila) da kuma Fatima Oloko (Abia Angels).
Masu tsaron baya kuma akwai Osinachi Ohale (Pachuca Tuzas, Mexico) da Michelle Alozie (Olivia Wynn, Amurka) da Shukurat Oladipo (AS Roma, Italiya) da Rofiat Imuran (London City Lionesses, Ingila) da Glory Ogbonna (FC Kiryat Gat, Isra’ila) daOluwatosin Demehin (Galatasaray Sportive, Turkiyya) da Sikiratu Isah (Bnot Netanya, Isra’ila) da kuma Christy Ucheibe (SL Benfica, Portugal).
‘Yan wasan tsakiya sun ne Rasheedat Ajibade (Paris Saint Germain, Faransa) da Halimatu Ayinde (BK Hacken, Sweden) da Deborah Abiodun (Washington Spirit, Amurka) da Toni Payne (Everton Ladies, Ingila) da Jennifer Echegini (Paris Saint Germain, Faransa).
Har ila yua, ‘yan wasan gaba sun haɗa da Asisat Oshoala (Al Hilal, Saudi Arabia) da Gift Monday (Washington Spirit, Amurka) da Esther Okoronkwo (AFC Toronto, Kanada) da Joy Omewa (BK Hacken, Sweden) da Francisca Ordega (Ittihad Ladies, Saudi Arabia) da Folashade Ijamilusi (Liaoning Shenyang Shenbei Hefeng, China) da Omorinsola Babajide (AS Roma, Italiya) da Chinwendu Ihezuo (Pachuca Tuzas, Mexico) da kuma Uchenna Kanu (Cruz Azul Femenil, Mexico).
