Tawagar ‘yan matan Najeriya ta Flamingos a ranar Alhamis, sun isa Lomé, ƙasar Togo, don fafata wasan ƙarshe da Jamhuriyyar Benin a wasan nemar tikin shiga Gasar Duniya ta 2026 da za a buga a ƙasar Moroko.

Bayan samun nasarar ci 3-2 mai cike da tashin hankali a Ikenne, a wasan zagayen farko, yanzu za a buga wasan zageye na biyu a ranar Asabar, inda Flamingos za ta kece ranin ƙarshe da Young Amazons na Jamhuriyar Benin a filin wasa na Stade de Kégué.

Duk da nasarar, kocin Flamingos Akeem Busari ya bayyana cewa tawagarsa dole ta sake inganta tsaron bayanta.

A gefe guda, kocin Benin, Idah Azonsou ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Young Amazons na da abin da za su iya yi don kafa tarihi domin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta Duniya a karon farko.

Ga Najeriya, lissafin yana da sauƙi.

Ko dai kunnen doki ko nasara a Lomé zai tabbatar da cancantar zuwa Moroko 2026, kuma zai ƙara bayyanar Flamingos karo na 9 a Gasar Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *