Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce kafa rundunar ‘yan sandan jihohi zai taimaka matuƙa wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya, domin hakan zai bai wa gwamnoni cikakken ikon gudanar da aikinsu a matsayin manyan jami’an tsaro na jihohinsu

Lawal ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a matsayin ɗaya daga cikin masu tattaunawa a taron Arise News Town Hall Summit mai taken: “Gina Matsaya Ta Ƙasa Kan ‘Yan Sandan Jihohi da Tsaron Ƙasa”, wanda aka gudanar a Thisday Dome da ke Abuja

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa daɗewar matsalar rashin tsaro a jihohi da dama ya samo asali ne daga rashin daidaito tsakanin nauyin da gwamnoni ke da shi da kuma ikon da suke da shi kan jami’an tsaro

A cewarsa, ana kiran gwamnoni manyan jami’an tsaro na jihohinsu, amma ba su da ikon umarni da kula da hukumomin tsaro da ke aiki a jihohinsu

Ya ƙara da cewa idan aka ba gwamnatocin jihohi cikakken alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, za a samar wa rundunar ‘yan sanda isassun kuɗaɗe da kayan aiki da kuma ƙarin jami’ai domin yaƙi da laifuffuka a matakin ƙasa.

“Lokacin da gwamnatocin jihohi suka ɗauki cikakken alhakin tsaron rayuka da dukiyoyi a yankunansu, rundunar ‘yan sanda za ta fi samun kayan aiki da ma’aikata da za su iya yaƙi da aikata laifuffuka yadda ya kamata,” in ji shi.

Da yake mayar da martani kan fargabar cewa wasu gwamnoni za su iya amfani da ‘yan sandan jihohi wajen muzgunawa ‘yan adawa, Lawal ya ce irin wannan tsoro ba shi da hujja a aikace.

Sai dai ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta kafa dokoki da matakan kariya domin hana duk wani yiwuwar amfani da rundunar ta hanyar da ba ta dace ba.

Muhawarar kafa ‘yan sandan jihohi ta sake ƙara ƙarfi sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da rikice-rikicen ƙabilanci a sassa daban-daban na ƙasar, inda gwamnoni da dama ke jaddada cewa tsarin ‘yan sanda na jihohi ne zai fi dacewa wajen hana aikata laifuffuka da tabbatar da tsaro a matakin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *