Shugaban ya bukaci majalisar ta gaggauta gyaran daftarin dokar ba tare da bata lokaci ba

Majalisar dattawa ta karanta wasikar da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike mata, game da gyaran dokokin da suka kafa hukumar dake kula da manyan Makarantun Sakandire ta Kasa (NSSEC).

Da ake karanto wasikar gaban zauren majalisar a ranar Alhamis, Shugaba Tinubu ya shaida wa mambobin majalisar cewa Majalisar zartarwa ta Kasa (FEC) ce ta amince da daftarin kudirin gyaran dokar, a taron  ta na ranar 30 ga Afrilu, 2026.

A cewar Shugaban kasar, dokar da ake shirin gyarawa na nufin kyautatawa tare da inganta ayyukan hukumar, da kuma inganta tsarin tafiyar da makarantun sakandire na gwamnati Nijeriya.

Tinubu ya kara da cewa wannan gyare-gyare sun yi dai-dai da kudirin gwamnatin sa, na gina ingantattun cibiyoyin ilimi domin kyautata harkokin koyo da koyar wa, da nufin farfado nagartar ilmi da cigaban kasa.

Bayan karanto wasikar, Godswill Akpabio ya mika daftarin kudirin ga Kwamitin dokoki na majalisar, domin nazari da kuma mika rahoton sa gaban zauren majalisar a cikin mako guda.

Ana sa ran gyaran dokar zai kai ga karawa hukumar karfin aiwatar wa da na gudanar wa ba tare da katsalandan daga bangarori dake hana wa mata ruwa gudu ba.

Matsayin Shugaban kasar na zuwa ne a wani lokaci da Makarantu masu zaman kansu ke cin kasuwa, sakamakon tabarbarewar harkokin ilmi a makarantun gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *