Najeriya ta samu damar karɓar bakuncin Gasar Cin Kofin Ƙwallon Ragar Rairayi Ta Afirka ta 2027, kamar yadda Hukumar Wasanni ta Ƙasa ta bayyana ranar Alhamis.
Hukumar ta tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Ƙwararrun Kwamitocin Olympics na Afirka ANOCA, Mustapha Berraf ya fitar a Abuja.
Berraf ya ce ANOCA ta ji daɗin ci gaban da aka samu a fannin wasanni a Najeriya kwanakin nan, wanda hakan ya sa suka gaggauta ba ta damar ɗaukar nauyin gasar ta 2027.
-
Flamingos sun isa Lomé don fafatawar ƙarshe da Benin a wasan nemar tikin shiga Gasar Duniya
-
Faransa 2-0 Moroko: Mbappe ya zura ƙwallo, ya bayar da taimako an ci guda
“Ina son in gode wa Gwamnatin Tarayyar Najeriya bisa abin da take yi a fannin wasanni a kwanakin nan. Shi ya sa ba mu daɗe ba muka ba Najeriya damar ɗaukar nauyin Gasar Cin Kofin Ƙwallon Raga ta Rairayi ta Afirka ta 2027,” in ji shi.
Da yake bayyana jin daɗinsa, Shugaban Hukumar Wasanni na Ƙasa, Shehu Dikko ya ce samun wannan damar wani babban ci gaba ne a cikin tsarin hukumar na bunkasa wasannin cikin gida.
Mista Dikko ya ce, “Mun ɗauki bunkasa tattalin arzikin wasannin ƙasar nan da muhimmanci. Ɗaya daga cikin hanyoyin cimma hakan shi ne janyo ƙarin gasa ta duniya zuwa Najeriya.”
Za a gudanar da gasar ne a Legas, inda ake sa ran hakan zai ƙara karfafa martabar Najeriya a matsayin wurin da ake gudanar da manyan gasa na nahiyar.