Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta kasar Farisa, wato Iran (IRGC) ta sanar da rufe mashigin ruwan Hormuz har sai abinda hali yayi.

Haka kuma ta kaddamar da hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da kawayenta a yankin.

IRGC ta ce ta kai hari kan wani sansanin sojojin Amurka da ke Jordan.

A lokaci guda kuma, kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Qatar da Kuwait da Bahrain sun ce sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka (drones) daga Iran.

Wannan na zuwa ne bayan wasu hare-hare da suka faru a farkon makon nan, inda aka kai hari kan jiragen ruwa masu daukar kayayyaki guda uku, lamarin da ya jawo musayar hare-hare tsakanin Amurka da Iran.

A yau Lahadi, kafafen yada labaran gwamnatin Iran sun bayyana cewa an rufe mashigin Hormuz har sai an sake sanarwa, bayan Iran ta harba makami mai linzami na ruwa kan wani jirgin ruwa da ke kokarin wucewa ta hanyar da ba a amince da ita ba.

Rundunar IRGC ta ce an yiwa jirgin harbin gargadi sannan aka dakatar da shi, bayan ya yi watsi da umarni da aka maimaita masa sau da dama, kamar yadda sanarwar da kamfanin dillancin labaran gwamnati ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *