Tawagar ‘yan matan Najeriya ‘yan ƙasa da shekaru 17, Flamingos, sun samu tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta mata ta bana bayan sun doke Amazons na Jamhuriyar Benin da ci 5-3 a Lome ranar Asabar.

Da wannan nasara, Flamingos ta haɗa jimillar ƙwallaye 8-5 a wasanni biyu na gida da waje da suka buga.

Da farko dai, tawagar Akeem Busari ta doke su da ci 3-2 a wasan farko da aka buga a Ikenne, Jihar Ogun.

Najeriya ta fara da kyakkyawan yanayi a Lome, inda Mary Dustan ta zura kwallo ta farko a minti na 6.

Sai dai masu masaukin baƙi sun farke ƙwallon minti 3 kacal bayan haka.

Flamingos suka sake samun nasarar jefa ƙwallo a minti na 15 ta hannun Esther Stephen, kafin Queen Joseph ta kara na uku bayan minti biyar.

Duk da yunƙurin da ‘yan Benin suka yi na komawa cikin wasan, flamingos sun daidaita kansu har zuwa ƙarshen wasan.

Queen Joseph ta zura ƙwallonta ta biyu a wasan a minti na 76, inda ta tabbatar da nasarar 5-3 wadda ta tabbatar wa Najeriya tikitin zuwa Moroko.

A yanzu Flamingos za su fafata tare da manyan ƙasashe a Gasar Cin Kofin Duniya ta mata ta 2026, yayin da suke fatan ci gaba da kara suna a matakin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *