Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana cewa hukumar za ta duba yiwuwar ƙara yawan ƙasashe da ke buga Gasar Cin Kofin Duniya zuwa 64 a gasar ta 2030.

Gasar Cin Kofin Duniya dai ta samu babban sauyi a shekarar 2026, inda adadin ƙasashen da ke buga gasar suka ƙaru daga 32 zuwa 48, kuma ƙasashen Amurka, Canada da Mexico suka ɗauki nauyinta.

Tsarin ƙasashe 32 ya kasance tun daga 1998 har zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022.

Infantino, Shugaban FIFA, ya tabbatar da cewa za a yi tattaunawa kan sabon tsarin da aka tsara bayan gasar wannan bazara.

“Gasar ƙasashe 64, wani abu ne da za mu duba mu tattauna a cikin kwamitocin da suka dace bayan wannan Gasar Cin Kofin Duniyar,” in ji Infantino a wata hira da ya yi da kafar sadarwa ta ƙasar Switzerland da Bluewin, kamar yadda jaridar the athletic ta ruwaito.

“Kowace ƙasa ya kamata a ba ta damar cika mafarkin shiga Gasar Cin Kofin Duniya. Idan ba ka ba ƙananan ƙasashe dama su shiga Gasar Cin Kofin Duniya ba, za su rasa ƙwarin gwiwar ci gaba da inganta kansu,” in ji shi.

A cewar Infantino, an samu nasara kaso ɗari cikin ɗari na ƙara yawan ƙasashen zuwa 48 a Gasar Cin Kofin Duniya” ta 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *