Koci Aliyu Zubairu

An naɗa tsohon kocin Najeriya na ‘yan ƙasa da shekaru 20, Aliyu Zubairu, a matsayin sabon kocin ƙungiyar ƙasar Sudan, Al Ahli Madani, kan kwantiragin shekaru biyu.

Aliyu ya maye gurbin Farouk Jabra, kuma ya zama sabon koci daga Najeriya da ya karɓi ragamar ƙungiyar na nahiyar Afirka.

An sanar da naɗin Zubairu ne sa’o’i kadan bayan ya tabbatar da rabuwa da ƙungiyar Telecom SC na gasar firimiya ta biyu ta ƙasar Masar bisa yardar juna.

Da yake jawabi bayan kammala yarjejeniyar zuwa Sudan, koci Zubairu ya ce wannan babbar dama ce gare shi a cikin aikinsa.

“Al Ahli Madani babbar ƙungiya ce mai tarihi. Ina fatan yin aiki tare da ‘yan wasa, da masu gudanarwa da magoya baya domin cimma burinmu, musamman yanzu da ƙungiyar ke shirin buga Gasar Cin Kofin Confederation ta CAF,” in ji Zubairu.

Wannan mataki wata babbar nasara ce ga Zubairu, wanda tarihin aikinsa na kociya ke ƙara girma a Afirka.

Tsohon kocin ya taɓa jagorantar Wikki Tourists da Gombe United da El-Kanemi Warriors a gasar Firimiya ta Najeriya, kafin ya kai ga komawa Telecom SC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *