Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta ayyana wani da ake zargi da jagorantar ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi, Nnamuka Kelvin Uchenna, wanda aka fi sani da Odogwu, tare da wasu mutum uku, a matsayin waɗanda hukumar ke nema ruwa a jallo.

A cewar NDLEA, kotun tarayya da ke Owerri a jihar Imo ce ta ba da umarnin ayyana mutanen bayan bincike ya danganta su da wata ɓoyayyar cibiyar da ake kera sinadarin methamphetamine a ƙaramar hukumar Njaba ta jihar Imo.

Hukumar ta ce jami’anta sun gano cibiyar ne a watan Fabrairun 2026, inda suka ƙwace kilo 18.4 na sinadarin methamphetamine tare da wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen sarrafa miyagun ƙwayoyi.

NDLEA ta ce binciken kimiyya ya gano cewa waɗanda ake nema sun tsere, yayin da ake ci gaba da farautarsu domin gurfanar da su a gaban kotu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *