Takaddama tsakanin Amurka da Iran ta ƙara tsananta bayan hare-haren da ɓangarorin biyu ke ci gaba da kai wa juna, lamarin da ya fara shafar wasu ƙasashen Gulf da kuma hanyoyin safarar mai na duniya.

Rundunar tsaron juyin juya hali ta Iran (IRGC) ta Iran ta ce ta kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan wuraren da ke da alaƙa da Amurka a Jordan, Bahrain da Kuwait, a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ta kai wa Iran karo na goma a jere.

A nata ɓangaren, Rundunar Sojin Amurka ta (CENTCOM) ta tabbatar da cewa dakarun ta sun kai farmaki kan rukunin wuraren ajiye makaman Iran na ƙarƙashin ƙasa kusa da birnin Tabriz, tare da ruguza matattarar na’urorin kariya na saman ruwa da cibiyoyin ba da umarni kusa da birnin Bushehr.

Rahotanni daga Jordan da Kuwait sun nuna cewa dakarun tsaron ƙasashen sun harbo wasu jiragen yaƙi marasa matuƙa da Iran ta harba, yayin da hukumomin Bahrain suka ce hare-haren sun haddasa matsaloli ga tsarin kula da zirga-zirgar jiragen sama a ƙasar.

A halin da ake ciki, rikicin ya bazu zuwa mashigin ruwan Hormuz, inda Rundunar IRGC ta ce ta kai hari kan wasu tankokin dakon mai da ta zarga da bin hanyar da babu tsaro.

Hukumar kula da tsaron ruwan Birtaniya (UKMTO) ta tabbatar da cewa wasu manyan jiragen dakon mai guda biyu sun kama da wuta a gabar tekun Oman, lamarin da ya tilasta wa ma’aikatansu barin jiragen domin tsira.

Haka kuma, mayakan Houthi na Yemen sun sanar da hana zirga-zirgar wasu jiragen ruwan kasuwanci zuwa tashoshin jiragen ruwa na Saudiyya, yayin da farashin danyen mai na Brent ya haura dala 90 kan kowace ganga sakamakon fargabar katse safarar mai ta mashigin Hormuz.

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ƙasar sa na cikin abin da ya kira “cikakken yaƙi da abokan gaba”, yayin da rahotanni ke nuna cewa ƙoƙarin shiga tsakani na dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta ya ci tura.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *