Flying Eagles ta Najeriya ta ƙuduri aniyar doke Black Satellites ta ƙasar Ghana a wasan su na farko na rukuni na B a gasar WAFU B U20 Championship da za a buga a birnin Yamoussoukro na Cote d’Ivoire a ranar Litinin.
Kocin Flying Eagles, Abdu Maikaba, ya bayyana cewa “Muna neman nasara kai tsaye a kan Ghana saboda manufar mu ita ce mu kare kofin da muke riƙe da shi. Dole ne mu fara neman nasara a wasannin mu tun daga rana ta farko har zuwa ƙarshe.”
Nasara a ranar Litinin za ta sanya zakarun Afirka sau 7,watau Najeriya, cikin kyakkyawan matsayi na shiga wasan kusa da na ƙarshe.
-
Gasar Ƙasashe Rainon Ingila ta 2026: Scotland ta doke Najeriya a wasan Kwando na Kujera
-
Anthony Joshua ya tuna da abokansa da suka rasu a Najeriya bayan ya doke Kristian Prenga
-
Super Falcons ta fitar da sabuwar rigarta mai taurari 10 kafin Gasar WAFCON ta 2026
Har ila yau, Najeriya za ta fafata da Togo da kuma Burkina Faso a wasannin rukuni na B mai ƙungiyoyi 4.
Super Eagles za ta buga wasan ta na biyu na rukunin a ranar 30 ga watan Yuli da ƙasar Togo a filin wasa na Lycée Scientifique de Yamoussoukro; kafin wasan ƙarshe na rukuni da Burkina Faso a ranar 2 ga watan Augusta.
