Daruruwan masu zanga-zanga sun gudanar da taro a garin Vogan na ƙasar Togo ranar Asabar, inda suka buƙaci gwamnati ta soke sabon kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a shekarar 2024 tare da dawo da tsohon kundin tsarin mulki.

An fara taron ne da bikin gargajiya na zuba hadaya, kafin shugabannin ‘yan adawa da magoya bayansu su rera taken ƙasar Togo.

Masu zanga-zangar sun riƙe alluna da kwalaye masu ɗauke da saƙonnin adawa da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin, yayin da taron ya samu halartar daruruwan magoya baya.

Sauye-sauyen da aka amince da su a shekararv2024 sun kafa tsarin mulkin majalisa, inda aka bai wa Shugaban Majalisar Ministoci cikakken ikon gudanar da mulkin ƙasa.

Tsohon shugaban ƙasar, Faure Gnassingbé, ne ke riƙe da wannan muƙami a halin yanzu.

Mai magana da yawun ƙungiyar farar hula ta Front Citoyen Togo Debout, David Dosseh, ya ce sauyin kundin tsarin mulkin haramtacce ne.

Ya ce, “Sauyin kundin tsarin mulkin da aka yi a Togo a shekarar 2024 ba bisa doka ba ne.

Juyin mulki ne ta hanyar kundin tsarin mulki, kuma al’ummar Togo ba za su taɓa amincewa da wannan cin zarafi ba.”

A watan da ya gabata, Kotun Shari’a ta ECOWAS ta yanke hukuncin cewa sauye-sauyen sun saɓa wa ƙa’idojin dimokuraɗiyya na ƙasar, tare da bayyana su a matsayin “sauyin gwamnati da ya saɓa wa kundin tsarin mulki.”

Ko da yake hukuncin kotun ba ya da ƙarfin tilasta aiwatarwa, jam’iyyun adawa na fatan zai ƙarfafa jama’a su ci gaba da neman sauyi.

Shugaban jam’iyyar Democratic Force for the Republic, Maitre Dodji Apevon, ya ce canji ba zai samu ba sai idan jama’a sun farka.

Faure Gnassingbé ya fara mulkin Togo tun shekara ta 2005.

A ƙarƙashin sabon kundin tsarin mulkin, Majalisar Dokoki na iya sake zaɓensa ba tare da iyaka ba a matsayin Shugaban Majalisar Ministoci.

Sabon kundin ya kuma rage ikon shugaban ƙasa, inda ya mayar da muƙamin na alama kawai, tare da iyakance wa’adinsa zuwa wa’adi guda na shekara shida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *