Ma’aikatar Tsaron Saudiyya ta bayyana a ranar Litinin cewa rundunar kare sararin samaniyar ƙasar ta yi nasarar kakkabo tare da lalata wasu jirage marasa matuƙa (drones) da suka yi yunƙurin kai hari kan matatun mai da ke Yankin Gabas na ƙasar da kuma birnin Riyadh.

Jaridar Arab News ta ruwaito cewa mai magana da yawun ma’aikatar yana cewa ƙungiyoyin mayaƙa masu samun goyon bayan Iran da ke Iraki ne suka harba waɗannan jirage marasa matuƙa.

Ya ƙara da cewa Saudiyya tana da cikakken haƙƙin kare kanta da muhimman cibiyoyinta, kuma tana da ’yancin mayar da martani a lokacin da ya dace da kuma wurin da ta ga ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *