Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa ba a kammala aikin Millennium Tower ba shi ne yawan kuɗin da ake buƙata, wanda ya haura Naira biliyan 400, yana mai cewa kasafin kuɗin FCT kaɗai ba zai iya ɗaukar nauyin aikin ba.
Wike ya bayyana haka ne yayin duba wasu manyan ayyukan more rayuwa da ake aiwatarwa a Abuja, inda ya ce gwamnatin tarayya na tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu domin a ayyana Millennium Tower a matsayin babban aikin ƙasa da cibiyar yawon buɗe ido, domin samun kuɗin da zai ba da damar kammala shi.
Ministan ya ce idan FCT ta karkata dukkan kuɗaɗenta wajen aikin Millennium Tower, hakan zai janyo tsaiko ga sauran muhimman ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a babban birnin tarayya.
- Mu muka amince da Hukumar bogi ba tare da bin ka’idar da aka shimfida ba–Shugabar Ma’aikatan Tarayya
- Komai daidai ne a siyasa—Shugaba Tinubu: Martanin ‘yan Adawa
A yayin ziyarar, Wike ya duba ci gaban aikin titin Collector CO1 da kuma titin Arterial N1, inda ya nuna gamsuwa da yadda ayyukan ke tafiya.
Mista Wike ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin FCT ta himmatu wajen kammala dukkan manyan ayyukan tituna da ake gudanarwa tare da miƙa su ga jama’a kafin ƙarshen shekarar 2026.
Ministan ya ƙara da cewa amincewar da kamfanonin gine-gine ke da ita ga gwamnati wajen biyan kuɗaɗensu ce ta sa ayyukan ke ci gaba ba tare da tangarda ba.
Ya yi kira ga mazauna Abuja su ci gaba da nuna haƙuri yayin da ake ci gaba da aiwatar da ayyukan raya birnin.