Yayin da yake karɓar Manyan Jagororin Cocin Katolika Ta Najeriya a fadar Shugaban Kasa dake Abuja, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ‘yin komai don cimma manufa ko buri, daidai ne a siyasa.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa: “Wadanda za su yi ƙoƙarin ƙwatar mulki a hannuna za su gwada. Za su yi ƙoƙari. Komai halal ne a siyasa, kuma kowa yana da daidaitacciyar dama.

Ba zan ba su wata dama da za su ji su wasu ne ba”. “A’a, za mu gwabza da juna ne har sai mun kai ga gaci. Wannan ita ce gaskiyar magana. Hakan shi ne daidai a siyasa,” in ji Shugaban Ƙasa ga jagororin cocin Katolika, ya kuma kare Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) daga zargin nuna bambanci.

Tinubu ya yi bayanin cewa, “INEC ba ta ɗauki ɓangare ba. Ba ta taɓa tsoratar da kowa ba, kuma ba za ta taɓa yin hakan ba. Idan ‘yan hamayyar siyasa suna kuka da tsoron banza, to suna tsoron inuwar kansu ne da kuma rashin tabbas a cikin tafiyar da suke tare da ita.”

“Wannan gwamnati ta daidaita ƙasa, kuma akwai yalwa da wadata a gaba. Yanayin rayuwa yana inganta,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa bai gudu daga nauyin yanke mawuyacin shawarwari ba.

Wannan kalamai da makaman na Shugaba Tinubu sun ta da kura sosai, domin jam’iyyun adawa ba su ji dadin su ba; abin da ya jawo martini mai zafi daga bangaensu.

Cikin jam’iyyun adawar da su ka mai da martini ga kalman na Shugaban na Najeriya akwai Jam’iyyar Allied People’s Movement (APM), inda ta fito fili ta musa ikirarin Shugaban na cewa ana samun kyautatuwar tattalin arziki da tsaro.

APM ta bakin Sakataren Yaɗa Labaranta na Ƙasa, Abubakar Yusuf, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce shugaban ƙasa yana ƙoƙarin nuna hoton abin da ba shi ne ke faruwa a ƙasar ba kawai, tana mam nuna cewa halin da ƙasar ke ciki bai sauya ba.

A cewar jam’iyyar hamayyar, binciken masu zaman kansu daga hukumomi masu sahihanci ya nuna cewa matakin talauci a ƙasar ya yi tashin gwauron zabi zuwa sama da kashi 63 cikin ɗari, inda fiye da rabin mutane miliyan 280 na al’ummar ƙasar abin ya shafa.

A na ta ɓangaren Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta soki shugaban saboda cewar da ya yi, zai yi “fada har zuwa karshe” a siyasa, a don haka, sai ta bukaci shugaban da ya fi mayar da hankali kan yaki da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane maimakon yaki da ‘yan adawa.

Ita kuwa jam’iyyar NDC, zargar shugaba Tinubu ta yi da cewa yana yunkurin ɗauke hankalin jama’a ne kawai daga muggan matsalolin tsaro da suke ci wa al’umma tuwo a kwarya, maimakon magance su.

Ba Jamiyyun adawa ne kaɗai suka mai da martini ga kalaman na Shugaba Tinubu ba; har fitattun ‘yan siyasa a na su bangaren, ba a bar su baya ba, inda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya nuna cewa ya kamata shugaban ya magance hauhawar farashin kayayyaki da yunwa da rashin tsaro, ba wai ya mayar da hankali kan tsoratar da abokan hamayya ba.

Shi ma ɗan takarar Shugabancin kasa na jam’iyyar NDC, Petre Obi, a na sa martanin bayan kalaman na shugaban kasa, ya bayyana cewa gwamnatin ta kasa shawo kan matsalolin tsaro da kuma tsadar rayuwa dake damun ‘yan kasa, ya kuma zargi shugaban da cewa yana yunkurin ɗauke hankalin jama’a daga muggan matsalolin tsaro.

Sai dai ita ma jam’iyya mai Mulki, APC, ta hannun Sakatarenta na Ƙasa, Ajibola Basiru, ta bayyana cewa jam’iyyar za ta yi nasara ko ma wanene ke jagorantar hukumar zaɓe, tana mai cewa kukan da ‘yan hamayya ke yi game da INEC ya samo asali ne daga tsoro da rauni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *