Wani binciken Majalisar Dinkin duniya ya nuna cewa matsin tattalin arziki ne ke kan gaba a abubuwan da matasa ke la’akari da su kafin su yi aure ko wata dangantaka ta soyayya. Kashi 81 cikin 100 na waɗanda aka yi wa tambayoyi sun ce samun kwanciyar hankali ta fuskar kuɗi na da matuƙar muhimmanci wajen kafa iyali.
Binciken ya kuma bayyana cewa matsalolin tattalin arziki da rashin isasshen muhalli su ne manyan ƙalubalen da ke hana Matasa yin aure ko zama tare da abokan rayuwa.
Sannan Kashi 57 cikin 100 sun bayyana waɗannan matsaloli a matsayin babban cikas. Duk da haka, fiye da kashi biyu bisa uku na binciken ya nuna ce wa har yanzu aure shi ne tsarin rayuwar iyali da suka fi so.
-
Mali: HRW ta zargi dakarun Africa Corps na Rasha da kashe fararen hula takwas
-
A karon farko an zabi mace ta shugabanci Majalisar Dokokin Aljeriya
Rahoton ya nuna cewa akwai matasa masu shekaru tsakanin 25 zuwa 39 da ke son yin aure ko zama tare da aboki/kiyar rayuwa, amma ba su da halin yin auren.
Kashi ɗaya bisa huɗu na waɗannan matasa ba sa soyayya kwata-kwata, inda adadin ya kai kashi 30 cikin 100 a tsakanin maza, yayin da kason mata ya tsaya kan kashi 19 cikin 100.
Dangane da haihuwa kuwa, binciken ya nuna cewa, mafi yawan matasa na ganin dole ne su samu wadataccen kuɗi, da aikin yi mai ɗorewa da kuma madafan dafawa kafin su zama iyaye. Haka kuma, kashi 72 cikin 100 sun ce matsin tattalin arziki da matsalar gidaje su ne manyan abubuwan da ke hana su haihuwa. Sai dai kashi 80 cikin 100 sun ce farin ciki da jin daɗin da yara ke kawowa iyali, babban abin da ke ƙarfafa su suga Suma sun haifi yara, ba wai manufofin gwamnati ba.
Har ila yau, mata sun fi maza bayyana cewa samun yara na buƙatar cika wasu muhimman sharuɗɗa da kuma shawo kan wasu ƙalubale kafin fara tara yara.