Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta sanar da wata gagarumar nasara da ƙasar nan ta samu, inda Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (ICAO) ta tabbatar da cewa ingancin filayen jiragen sama na Najeriya ya haura matsayin da ake buƙata a duniya.
A wata sanarwa da FAAN ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Juma’a, ta bayyana cewa makin da Najeriya take da shi wajen cika ƙa’idodin tsaro da ingancin aiki ya tashi daga kashi 70.23 cikin 100 zuwa kashi 91.45 cikin 100.
Wannan matsayi ya sa Najeriya ta tsallake matsakaicin matsayi na duniya wanda yake da kashi 70.4 cikin 100.
- Minista ya roki masu kamfanonin jiragen sama da kada su daina aiki
- Kamfanin jirgin sama na KLM ya soke tashin jirage 160
- Abubuwa 5 da Taiwo Oyodele zai baiwa muhimmanci
Dukkan filayen jiragen sama na duniya suna samun shaidar inganci amma wanna
n shi ne karo na farko da dukkanin filayen jiragen saman Najeriya guda biyar da ke karbar jirage masu zirga-zirgar ƙasa da ƙasa suka samu cikakkiyar takardar shaidar inganci daga ICAO.
FAAN ta ce nasarar ta kammala ne bayan da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta ba da wata takardar shaida ga filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Enugu, bayan daukaka darajarsa zuwa na kasa-da-kasa a shekarar 2010.
Maki da Najeriya ke da shi a fannin kula da filaye ya tashi daga kashi 57.5 cikin 100 a shekarar 2023 zuwa kashi 95.16 cikin 100 a halin yanzu.
Najeriya ta shiga jerin kashi 50 cikin 100 na kasashen nahiyar Afirka da suka samu irin wannan shaida, wadda ke samuwa bisa la’akari da kyautata yanayin filayen sauka da tashi, sai horar da ma’aikata, da kuma tabbatar da cikakken tsaro.
Ɓangaren na sufurin jiragen sama a Najeriya na fuskantar matsin lamba na asarar da yake yi a kasuwancinsa, sakamakon matsalar hauhawar farashin man jirgi, wanda yakin Iran da Isra’ila ya haifar.
Wannan mataki ya kusan sanya kamfanonin dakatar da ayyukan su har sai al’amura sun daidaita a ɓangaren na farashin mai, gabanin gwamnatin kasar ta roke su da su jingine tare da kai zuciya nesa.
