Kyaftin din kungiyar Manchester United, Bruno Fernandes.

Kyaftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes, ba na sayarwa ba ne a ko wane irin farashi, duk da sha’awar da Galatasaray ke nunawa akan ɗan wasan.

Rahotanni sun ce ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya na shirin taya ɗan wasan mai shekaru 31, wanda ya shiga shekara ta ƙarshe a kwantiraginsa, amma United na da damar ƙara masa kwangilar shekara guda.

United ba za ta saurari wani tayi ba akan ƙwararren ɗan wasan, wanda tuni kwantiragin sa na fam miliyan 57 a matsayin sharaɗin sayar da shi daga ƙungiyar ya ƙare.

Har yanzu dai babu wani batu a hukumance kan ƙara wa’adin kwangilar tasa.

Majiyoyin ƙungiyar sun ce, har yanzu babu wani tayi da aka yiwa ɗan wasan mai shekaru 31, amma sun ƙara da cewa ba za a sayar da shi ba ko da a wanne irin farashi ne.

A watan Disamba, Fernandes ya bayyana cewa ya ji “takaici” lokacin da United ta gaya masa a bazarar da ta gabata cewa yana iya karɓar babban tayi daga ƙungiyar Al Hilar ta Saudiyya, wanda suka shirya sayen sa akan ƙudi fam miliyan 100.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *