Kanada za ta sanar da matakan ramuwar gayya kan Amurka a yau Talata, yayin da dangantakar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara tabarbarewa.
Hakan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara matsa wa shugabannin Kanada lamba, yana mai cewa su “bi layi” ko kuma su fuskanci matakan da suka fi harajin da ake ciki tsanani.
Firaministan Kanada Mark Carney ya zargi gwamnatin Amurka da ƙoƙarin mayar da ƙasar ƙarƙashin ikon Washington, yayin da Ottawa ke shirin ɗaukar matakan mayar da martani kan manufofin harajin Trump.
- Kanada za ta sanya harajin kayayyaki kan Amurka
- Yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka ita ce hanya mafi dacewa—Pezeshkian
- Barazanar Trump ta Illata Kasuwannin hannun jarin Amurka
Ana sa ran matakan Kanada za su shafi wasu kayayyakin Amurka, lamarin da zai iya ƙara faɗaɗa takaddamar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Rikicin ya samo asali ne daga matakan harajin da gwamnatin Trump ta ƙaƙaba wa wasu kayayyakin da ake shigowa da su Amurka. Kanada ta yi adawa da matakan, tana mai cewa za su iya cutar da kasuwanci da tattalin arzikin ƙasashen biyu.
A nata ɓangaren, gwamnatin Trump ta kare manufofin harajin da ta ɗauka, inda ta ce matakan na da muhimmanci wajen kare masana’antun Amurka da kuma daidaita harkokin kasuwanci.
Masana tattalin arziki na gargadin cewa idan ɓangarorin biyu suka ci gaba da ƙara haraji, hakan na iya janyo tashin farashin kayayyaki, rage cinikayya da kuma kawo cikas ga kamfanonin da suka dogara da samar da kayayyaki tsakanin ƙasashen biyu.
Kanada da Amurka na da doguwar dangantakar kasuwanci, don haka wannan sabon rikicin na iya shafar masana’antu, ‘yan kasuwa da masu amfani da kayayyaki a ƙasashen biyu.
Ana sa ran sanarwar Kanada a yau Talata, inda za ta fayyace irin matakan da Ottawa za ta ɗauka, sai Kuma mu jira bangaren gwamnatin Trump ko za ta ɗauki wani sabon mataki na mayar da martani.