Ministan Harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan, ya jaddada buƙatar samun haɗin kan Musulmi yayin da ake fuskantar ƙalubale a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron Majalisar Ministocin Harkokin waje, na Ƙungiyar haɗin kan Musulunci (OIC).
- Hukumomi a Jamus na binciken asalin kasar da wani Sauro ya fito bayan mutuwar Ma’aikatan jirgi
- Dandalin Adzuna ya ce gurbin aikin yi ga masu shaidar digiri ya ragu a Birtaniya
- An dakatar da wasu wakoki daga shiga jerin fitattun wakoki a Ostreliya sakamakon amfani da AI
Bin Farhan ya sake tabbatar da goyon bayan kasar Saudiyya na dogon lokaci ga ƙudurin samar da kasar Falasɗinu, tare da yin Allah-wadai da yawan kutsen da ake yi a Masallacin Ƙudus.
Haka kuma, ya bayyana goyon bayan sa ga ƙarfafa Ƙungiyar Haɗin Kan Musulunci (OIC) da kuma habbaka rawar da take takawa wajen tunkarar ƙalubalen da ke addabar yankin.