Dakarun Sojojin Najeriya tare da wata tawagar musamman sun hallaka ’yan ta’addan Boko Haram 21 a wani samame da suka kai kan sansanin ’yan ta’addan da ke yankin tsaunin Kopre, a ƙaramar hukumar Hong da ke jihar Adamawa.
An gudanar da aikin ne tsakanin safiyar ranar 26 zuwa 27 ga watan Agusta, bayan da dakarun suka samu ingantaccen bayanan sirri kan kasancewar ’yan Boko Haram a yankin.
Majiyoyin soji sun shaida wa Zagazola Makama cewa bayan samun bayanan, dakarun sun yi kutsen sirri zuwa yankin daga ƙarfe 1:30 na dare na ranar 26 ga Agusta zuwa ƙarfe 4:10 na asubahin ranar 27 ga Agusta, inda daga bisani suka kai farmaki kan sansanin ’yan ta’addan da ke kusa da tsaunin Kopre.
- Tinubu ya umurci a yi cikakken garambawul a harkar ƙwallon ƙafa ta Najeriya
- Ambaliya a Nepal da Tibet ta kashe Mutane sama da 270
- Yan Najeriya 67 sun dawo daga Afirika ta Kudu
Majiyoyin sun ce harin ya yi sanadin mutuwar ’yan Boko Haram 21, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Dakarun sun kuma lalata sansanin ’yan ta’addan tare da kayan aikinsu na yaƙi da sauran kayayyakin da aka samu a wurin.
An kwato makamai da alburusai da dama, ciki har da bindigogi kirar AK-47, kwanson harsashin bindiga AK-47 da kuma alburusai nau’in 7.62mm.
Haka kuma, dakarun sun lalata babura da dama da kekuna da kuma jarkunan man fetur (PMS) mallakar ’yan ta’addan.
Rundunar sojin ta ƙara bayyana cewa wani jami’in ’yan farauta (hunters) da ke taimakawa wajen gudanar da aikin ya rasa ransa yayin arangamar.
Ba a samu rahoton asarar kayan aikin soji ba.
Wannan sabon samame na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin dakarun Operation Hadin Kai na dakile ayyukan ta’addanci tare da hana ’yan Boko Haram damar yawo cikin ’yanci da samun kayan tallafi a wasu sassan jihar Adamawa.