Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta yi kira da a ƙara zuba jari a cikin fasahohin da ake ƙerawa a cikin gida, domin rage dogaro da manhajojin ƙasashen waje domin samar wa bangaren ‘yanci.
Mataimakin Shugaban Hukumar NCC, Aminu Maida, ne ya yi wannan kiran a ranar Alhamis yayin bikin rufe gasar ginin sabbin manhajoji da hukumar ta shirya karo na huɗu da aka gudanar a Abuja.
A yayin taron, masu ƙirƙire-ƙirƙire sun gabatar da hanyoyin fasaha da aka samar domin taimaka wa masu nakasa da sauran ‘yan Najeriya da ke fuskantar ƙalubalen samun damar amfani da fasahar ƙirƙira.
- Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’addan Boko Haram 21, Sun Lalata Sansaninsu a Adamawa
- Tinubu ya umurci a yi cikakken garambawul a harkar ƙwallon ƙafa ta Najeriya
- Mu haɗu a kotu: VeryDarkMan ya mayar wa ‘yan sanda martani
Maida, wanda Kwamishiniya mai kula da Hulɗa da Masu Ruwa da Tsaki, Rimini Makama, ta wakilta, ya ce dole ne Najeriya ta daina kasancewa ƙasa da ke dogaro da manhajojin da ake shigo da su daga ƙasashen waje, ta koma ga samar da fasahohin da suka dace da bukatun al’ummar ƙasar.
Ya ƙara da cewa sababbin fasahohin da aka samar a gasar, waɗanda suka haɗa da fasahar zamani ta AI mai sauya magana zuwa rubutu, shafukan gwamnati masu aiki da murya, hanyoyin tura sakonnin da kuma manhajojin wayar hannu da nakasassu ke amfani dasu, na daga cikin tubalan da za su taimaka wajen samun dogaro da kai a fannin fasaha.
Shugaban na NCC, ya kuma yi kira ga masu zuba jari na kamfanonin sadarwa da gwamnatocin jihohi da su samar da jari, da haɗin gwiwar da ake buƙata domin a fitar da waɗannan sabbin fasahohin daga matakin gwaji zuwa amfani na zahiri.