Abel Olumuyiwa Enitan, shine sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar a wannan makon.

An nada Mista Enitan ne bayan ritayar Didi Walson-Jack.

Ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da mutumin da zai jagoranci ma’aikatan Gwamnatin Tarayya sama da 600,000 a ma’aikatu da hukumomi fiye da 500:

Rayuwarsa

An haifi Mista Enitan a ranar 12 ga watan Disamba, 1966, kuma dan asalin jihar Osun ne.

Ya shafe kusan shekaru 30 yana aiki a ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, inda ya rike mukamai daban-daban kafin a daga likkafar sa zuwa matsayin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati.

Kafin nadin nasa, Mista Enitan ne Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, sannan kuma shi ne babban ma’aikacin gwamnati mafi dadewa a wannan matsayi.

Matakin Karatu

Abel Olumuyiwa Enitan ya yi karatunsa na sakandare a Ajibode Grammar School da ke Birnin Badin, sannan ya wuce Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ile-Ife.

Daga nan ya yi karatu a Jami’ar Legas, inda ya samu digirinsa na farko a fannin Aikin Banki da Sarrafa Kudade a shekarar 1988.

A shekarar 2015 kuma ya samu digiri na biyu a fannin Nazarin Manufofin Gwamnati daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi.

Aikin Gwamnati

Mista Enitan ya fara aiki da Gwamnatin Tarayya a shekarar 1998, inda ya fara aiki a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa tare da tsohuwar Hukumar Tattalin Iyali (FEAP).

Daga baya ya yi aiki a Ma’aikatar Bunkasa Yankin Neja Delta, kafin ya koma Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa.

A Fadar Shugaban Kasa, ya yi aiki a matsayin Babban Jami’in Mulki, sannan ya samu karin girma zuwa matsayin Darakta, mukamin da ya rike daga shekarar 2010 zuwa 2018.

A watan Disamba na shekarar 2018 ne aka nada shi Babban Sakatare.

Tun daga lokacin, ya rike mukamai a wasu muhimman ma’aikatu da hukumomin gwamnati wadanda suka hada da:

•⁠ ⁠Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

•⁠ ⁠Ma’aikatar Muhalli

•⁠ ⁠Ma’aikatar Harkokin ’Yan Sanda

•⁠ ⁠Ma’aikatar Harkokin Jinkai da Rage Talauci

•⁠ ⁠Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, da

•⁠ ⁠Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

Kafin nadinsa a matsayin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Enitan ya shafe kusan shekara bakwai da wata bakwai yana rike da mukamin Babban Sakataren Ma’aikatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *