Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa Luanda, Angola, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron musamman karo na 21 na Majalisar Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Mataimakin Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Stanley Nkowcha, ya fitar, ya ce babban taron zai mayar da hankali ne kan muhimman dabarun warware rikice-rikice da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a nahiyar Afirka.
- Sojoji sun kama masu taimaka wa ’yan ta’adda 3, sun lalata maboyarsu a Kaduna da Katsina
- Tinubu ya shigar da ƙara kotun Amurka don hana fitar da takardun zargin safarar miyagun ƙwayoyi
- Mallakar makamai ba bisa ka’ida ba: Kotu ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kwanaki 250 a gidan gyaran hali
Sanarwar ta ce Mataimakin Shugaban Ƙasar zai haɗu da shugabannin ƙasashen Afirka da sauran masu ruwa da tsaki da za su taru a Luanda domin tattauna hanyoyin magance ƙalubalen tsaro da suka addabi yankuna daban-daban, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen Afirka wajen hana rikice-rikice da warware su.
An bayyana cewa Najeriya, wadda ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da warware rikice-rikice a Afirka da sauran sassan duniya, za ta bayar da gudunmawa wajen tattaunawa kan hanyoyin ƙarfafa tsarin nahiyar na hana rikici, sasanta saɓani da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.