Rayuwa ta koma yadda take a birnin Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar, ranar Lahadi bayan da gwamnatin sojin ƙasar ta dakile wani yunkurin tawaye da wasu sojoji suka yi a ranar Asabar.

An yi musayar wuta mai tsanani da sanyin safiyar Asabar, inda rahotanni suka ce an kama sojoji da dama bayan sun yi yunkurin mamaye fadar shugaban ƙasa.

Wasu kuma sun rasa rayukansu yayin da suke koƙarin shiga fadar.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin sojojin sun nuna rashin gamsuwa kan yadda gwamnati ta gaza dakile hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar.

Wannan ne karo na uku da aka samu rikici a birnin Niamey a cikin wannan shekara.

Sai dai rikice-rikicen biyu da suka gabata sun shafi hare-haren da mayakan jihadi suka kai kan wani muhimmin sansanin soja da ke filin jirgin saman birnin.

Wani mazaunin Niamey mai suna Hassane Assoumane ya ce duk lokacin da aka samu tawaye a cikin rundunar soja, hakan na nuna cewa akwai matsaloli da ya kamata gwamnati ta magance.

Ya ce yana kan hukumomi su nemo mafita, ko ta hanyar tattaunawa da masu tayar da kayar baya ko kuma ta wata hanya daban.

Janar Abdourahmane Tiani ya karbi mulkin Nijar ne bayan juyin mulki da ya yi shekaru uku da suka gabata, inda ya yi alkawarin inganta tsaro.

Amma gwamnatin tasa na ci gaba da fuskantar kalubale wajen dakile hare-haren kungiyoyin da ke da alaka da kungiyar Da’esh da Al-Qaeda.

Bayan raba gari da tsohuwar kasar mulkin mallaka ta Faransa, gwamnatin Nijar ta kara kusanci da kasashe irin su Rasha, Turkiyya da Iran. Rahotanni sun ce dakarun kungiyar Africa Corps ta Rasha sun taimaka wajen dakile yunkurin tawayen da aka yi a ranar Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *