Darakta-Janar na Cibiyar Kula da Yaduwar Ƙananan Makamai da Masu Sauƙin Ɗauka (NCCSALW), DIG Johnson Kokumo (mai ritaya), ya karyata wani zargi da ke yawo a wani bidiyo cewa Mai baiwa Shugaban Ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya dauki nauyin mutanen da aka kama bayan gano makamai a babbar tashar ruwa ta Tin Can Island dake Legas.

Kokumo ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, yayin wani taron haɗin gwiwa na masu magana da yawun hukumomin tsaro.

Ya ce shi da kansa yana tashar lokacin da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta miƙa wa cibiyar makamai masu sarrafa kansu guda 399 da aka kama a tashar.

Kokumo ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da lalata makaman da aka kwato domin hana su sake komawa hannun masu aikata laifuka da sauran ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba.

Ya ce lalata makaman na cikin yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa da Najeriya ta sanya hannu, na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), da Tarayyar Afirka (AU) da kuma ECOWAS.

A watan Yunin 2026, cibiyar ta kwace makamai da yawan su yakiai  dubu 5 daga rundunar ’yan sandan Najeriya, bayan da aka samu nasarar kwato su daga masu ta’ammali da rikewa ba bisa ka’ida ba.

Bayan wadanda aka kwato, akwai karin makamai da suka rigaya suka lalace da tsaffi da suka daina aiki da waɗanda aka daina amfani da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *