Jam’iyyar PDP tsagin Kabiru Tanimu Turaki ya amince da shirin G-100 na haɗakar jam’iyyun adawa domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na na tsagin Ini Ememobong, ya fitar a ranar Talata, bayan da jam iyyar ta gudanar da taron ta farko, wanda ya gudana a ranar Litinin a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.
Taron ya haɗa da wakilan jam’iyyun adawa domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa da kuma yiwuwar gabatar da ɗan takara guda ɗaya da zai fafata da jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
- Asusun X na Rundunar Sojin Najeriya ya sake fuskantar kutse
- EFCC ta kori ma’aikata fiye da 40
- Babu wata ƙungiyar addinin musulunci da ta ce za ta kafa Hisbah a Jihar Filato – JNI
Tsagin na PDP ya ce matakin shiga shirin ya samo asali ne daga abin da ya bayyanar wahalar da ’yan Najeriya ke sha ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Taron na G-100, wanda wakilan jam’iyyun adawa shida suka halarta, ya amince da fara tattaunawa a hukumance kan haɗin gwiwar jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Jam’iyyun sun amince da kafa kwamitoci na dindindin domin fitar da shawarwari kan makomar ‘yan adawar, wani sabon shirin gyaran ƙasa da kuma taswirar da za ta kai ga zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya.
Matakin na zuwa ne yayin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin kauce wa maimaita abin da ya faru a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, lokacin da rabuwar kai tsakanin ’yan takara ya janyo musu shan mummunan kaye.
Abinda ya ragewa gamayyar yan adawar shine ko zasu kai ga cimma matsaya yayin da zabukan kasar ke karatowa gadan-gadan.