Satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron Najeriya, yayin da rahotanni ke nuna cewa dubban mutane sun fada hannun masu garkuwa a cikin watanni 12 da suka gabata.
Wani rahoton cibiyar bincike ta SBM Intelligence ya gano cewa an sace mutane 7,825 tsakanin Yuli 2025 da Yuni 2026, yayin da akalla mutane 1,142 suka rasa rayukansu a hare-haren da suka shafi garkuwa da mutane. An kuma tabbatar da biyan sama da naira biliyan 7 a matsayin kudin fansa.
A farkon shekarar 2026 ma, matsalar ta ci gaba da kamari inda Amnesty International ta ce akalla mutane 1,100 aka sace a arewacin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu, dasuka hadar da mata, yara, manoma da wadanda ke wuraren ibada.
Daga cikin manyan hare-haren akwai wanda aka kai a Jihar Borno, inda aka ruwaito sace daruruwan mutane, da kuma hare-haren da aka kai a jihohin Kaduna, Kwara, Zamfara da Neja.
- An kammala taro kan tsaro tsakanin Najeriya da Turkiyya
- Babban Hafsan Tsaron Najeriya ya ce haɗin gwiwa da Saudiyya zai inganta harkokin tsaro
- ‘Yan sanda sun tsare jami’an tsaron Gwamnan Katsina a Abuja
Sai dai jami’an tsaro sun samu nasarar kubutar da wasu daga ciki inda a watan Agusta, gwamnati ta sanar da ceto mutane 308 a jihohin Neja da Kwara, ciki har da wasu da aka sace a harin Woro na Jihar Kwara.
A wani sabon hari a Jihar Neja kuwa, an ruwaito cewa kimanin mutane 600 aka yi garkuwa da su, yayin da akalla mutane 30 suka rasa rayukansu. Sai dai ana ci gaba da tantance ainihin adadin wadanda aka sace.
Masana tsaro na danganta yawaitar satar mutane da yaduwar makamai, raunin tsaro a wasu yankunan karkara da kuma yadda kudin fansa ya zama hanyar samun kudade ga masu aikata muggan laifuka.
Duk da haka, har yanzu babu cikakkiyar kididdiga da ta da ta tabbatar da jimillar mutanen da aka sace, ko aka kubutar da kuma wadanda suka mutu, daga Janairu zuwa Satumbar 2026.
Alkaluman hukumomi da kungiyoyin bincike sun bambanta saboda hanyoyin tattara bayanai da kuma hare-haren da ba sa samun rahoto a hukumance.
Yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ayyukan ceto da farautar masu garkuwa, matsalar na ci gaba da shafar rayuwar jama’a, tattalin arziki da tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.