Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ce ta ceto sama da yara 180 da ake zargin ƙungiyoyin masu aikata laifuka suka yi safarar su daga jihohi biyar na Najeriya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Vincent Adekoye, Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na NAPTIP, ya fitar a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, wasu ƙungiyoyin masu aikata laifuka na fakewa da sunan ƙungiyoyin fararen hula (CSOs) wajen yaudarar iyaye a al’ummomin da ke fama da matsalar tsaro, inda suke kwashe ’ya’yansu bisa alkawarin samar musu da ilimi da sauran tallafi.

Sanarwar ta ce sabon samamen da NAPTIP ta gudanar ya kai ga ceto yara uku da ake zargin an kwashe daga wani mahaifi da ke Kajuru, Jihar Kaduna, sannan aka kai su wani katafaren gini da ke Onitsha, Jihar Anambra.

Haka kuma, jami’an hukumar sun gano wani yaro a hannun wata ma’aikaciyar jinya da ke aiki a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Onitsha.

NAPTIP ta ce ƙungiyoyin da ake zargi suna amfani da shirye-shiryen tallafa wa ilimi da komawar yara makaranta wajen samun amincewar iyalan da rikici ya shafa, kafin su kwashe yaran daga hannun iyayensu.

Darakta-Janar ta NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta nuna damuwa kan lamarin, inda ta yi kira ga ƙungiyar da ke wakiltar ƙungiyoyin fararen hula a Najeriya da ta gudanar da bincike a cikin ƙungiyoyinta tare da fallasa mutanen da ake zargi da hannu wajen safarar yara.

Ta ce NAPTIP ta fara farautar mutanen da aka gano a cikin binciken, tare da yin alkawarin cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Hukumar ta ce ta kafa wata tawaga ta musamman a cikin Sashen Bincike da Sa-Ido domin binciken rahotannin bacewar yara, ceto waɗanda aka yi safarar su da kuma kamo waɗanda ke da hannu a aikata laifin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *