Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da ƙaruwar tattalin arzikin Najeriya, da yakaru a zango na biyu na shekarar 2026, inda ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa ya fara haifar da sakamako mai kyau.

Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 4.43 cikin 100 a watanni ukun da suka ƙare a watan Yunin 2026, idan aka kwatanta da kashi 4.23 cikin 100 da aka samu a makamancin lokacin na shekarar 2025.

NBS ta ce an samu ci gaba a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasar, ciki har da noma, da masana’antu, da man fetur da iskar gas, da kuma ɓangaren ayyuka, wanda ya kasance mafi girma daga cikin abubuwan dake baiwa kudaden shiga kwarin gwiwa.

 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar a Abuja ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya ce alkaluman na baya-bayan nan sun nuna cewa ajandar Renewed Hope ta gwamnatinsa na samar da sakamako da zai iya zama ma’auna.

Darajar kuɗaɗen shigar Najeriya ya kai naira tiriliyan 119.27 a zango na biyu na 2026, wanda ke nuna ƙaruwar kaso 18.43 cikin 100 daga naira tiriliyan 100.7 da aka samu a bara.

Shugaban ya ce, ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da wasu ke sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatinsa, suna cewa sun ƙara tsananta yanayin rayuwar jama’a.

“Ba mu aiwatar da sauye-sauyen nan ne domin haifar da ƙalubale ba, sai dai domin tabbatar da cewa wadata ta isa ga dukkanin al’ummar mu,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya kuma yi nuni da cewa ƙarin darajar Najeriya a idon hukumomin tantance darajar bashi, da kuma ayyukan gina tituna, layukan dogo da manyan hanyoyi, na daga cikin alamomin cewa tattalin arzikin ƙasar na samun sauyi.

Shugaba Tinubu ya ce ana kuma samun ƙarin masu zuba jari da ke dawowa Najeriya, yayin da ake samun ƙaruwa a yawan man fetur da iskar gas da ake hakowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *