Ma’aikatar Kuɗin ta tarayya ta ce tattalin arzikin Najeriya na ci gaba da ƙaruwa, bayan alkaluman kashi na biyu na shekarar 2026 sun nuna cewa ainihin GDP ya karu da kashi 4.43 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2025.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar a Abuja ta ce wannan ƙaruwa ya haɓaka matsakaicin ci gaban tattalin arzikin ƙasar a rabin farko na shekarar 2026 zuwa kashi 4.16 cikin 100, daga kashi 3.68 cikin 100 da aka samu a rabin farko na shekarar 2025.

Ma’aikatar ta ce ci gaban ya fara bazuwa zuwa sassa daban-daban na tattalin arziki, inda ƙananan sassa 27 suka samu ci gaban sama da kashi 3 cikin 100 a kashi na biyu na shekarar, sabanin 23 a makamancin lokacin bara.

A bangaren masana’antu, masana’antu sun samu ci gaban kashi 3.24 cikin 100, yayin da noma ya karu da kashi 4.39 cikin 100. Bangaren ayyuka kuwa, wanda shi ne mafi girman ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar, ya samu ci gaban kashi 4.60 cikin 100.

Ma’aikatar ta kuma ce darajar naira ta samu ɗan ƙarfafa, inda ta nuna cewa naira ta ƙaru da sama da kashi 12 cikin 100 tsakanin rabin farko na shekarar 2025 da na 2026.

A cewarta, hakan ya taimaka wajen haɓaka girman tattalin arzikin Najeriya da kusan kashi 17 cikin 100 idan aka auna shi da dalar Amurka.

Gwamnatin Tarayya ta ce idan aka ci gaba da samun daidaiton tattalin arziki, da ƙaruwa a sassan samar da kaya da ayyuka da kuma ingantaccen yanayin saka hannun jari, Najeriya na da damar ci gaba da rike matsayinta cikin manyan tattalin arzikin Afirka tare da cimma burin gina tattalin arzikin da darajarsa ta kai dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030.

Sai dai gwamnatin ta jaddada cewa akwai buƙatar ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki tare da tabbatar da daidaiton manufofi, domin fa’idodin ci gaban tattalin arzikin su isa ga gidajen al’umma.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *