Kwamitin Majalisar Wakilai ya wanke shugaban ma’aikatan fadar shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, daga zargin da hannunsa a cikin ayyukan ma’aikatar bogi ta PFIPC.
Kwamitin wucin gadi na majalisar da ke binciken yadda aka saka sunan hukumar a cikin kasafin kuɗin Gwamnatin Tarayya ya ce bai ga wata shaida da ke nuna cewa Gbajabiamila ya amince, ko kuma yana da masaniya akan kafa hukumar bogin ba.
Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin da yake gabatar da rahoton farko na kwamitin a yayin taron manema labarai.
-
Soji sun kwato makamai a Binuwai
-
Yadda ƙungiyoyin fararen hula suka gudanar da gangamin goyon bayan janar Tiani
-
NELFUND: Atiku ya yi alkawarin yafe bashi ga daliban Najeriya
Gagdi ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa Gbajabiamila ne ya kai rahoton hukumar ga hukumomin tsaro da na bincike yayin da aka kawo batun gabansa.
A cewar Gagdi, Kwamitin Hukumar jari na Najeriya ne ya fara shigar da ƙara, kan zargin zamba da kuma zargin amfani da takardun gwamnati ba bisa ka’ida ba.
A cewar kwamitin, shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasan ya mayar da martani cikin sa’o’i 24, ta hanyar tuntuɓar Rundunar ‘yan sanda, da ofishin mai bayar da shawara kan tsaro, da kuma hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS da kuma hukumar EFCC.
Yayin da bincike kan hukumar ta bogi ke ci gaba, Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta kai ga gano ƙarin wasu hukumomin na bogi, inda hakan ya ƙara haifar da tambayoyi kan yadda ake cigaba da samun hukumomin gwamnati na bogi da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba.
