Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sake duba tsarin Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) tare da yiwuwar yafewa wa wasu ɗalibai bashin karatun da suka ci.
Babban Mataimaki na Musamman na Atiku kan Sadarwar, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Talata.
Shaibu ya ce matakin na Atiku martani ne ga wani saƙon da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya wallafa a shafinsa na X, inda ya soki wasu shawarwarin tattalin arzikin Atiku ba tare da ambaton sunansa kai tsaye ba.
- Kamfanin Uber ya daina aiki a Najeriya
- Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda, sun kama albarusai masu yawa
- Ba aikin Dan sanda ba ne hana yawon Shanu a Abuja – CSP Ani Iniedu
Shaibu ya bayyana yadda Tinubu ya ambaci NELFUND a matsayin wata hujja da ke nuna cewa ilimi ya zama mai sauƙin biya a ƙarƙashin gwamnatinsa a matsayin “rashin gaskiya”.
Ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayya ta bari kuɗin makaranta ya ƙaru a wasu cibiyoyin ilimi kafin daga bisani ta ƙaddamar da lamunin ɗalibai domin taimaka musu wajen biyan ƙarin kuɗaɗen karatu.
A cewar Shaibu, Atiku ya sake nazarin tsarin lamunin ɗalibai na yanzu, kuma ya yi imanin cewa bai kamata matasan Najeriya su fara rayuwar aiki suna ɗauke da nauyin bashin karatun jami’a ba.
Ya ce tsarin da Atiku ke son aiwatarwa zai mayar da hankali wajen rage ainihin kuɗin karatu, tare da duba yiwuwar gafarta bashin lamunin karatu ga ɗaliban da suka cancanta.
Ya kuma ce rage farashin makamashi da sufuri zai ƙara wa ma’aikata ƙarfin saye, tare da rage kuɗaɗen da iyalai ke kashewa wajen sufuri da sauran muhimman bukatun yau da kullum.
A cewarsa, bai kamata gwamnati ta ƙara tsadar rayuwa, ta tilasta wa ɗalibai neman bashi, sannan daga bisani ta yi gargadin cewa rage farashin makamashi zai iya yin barazana ga samun lamunin karatu.
Shaibu ya ce manufar Atiku ita ce rage matsin tattalin arzikin da ɗalibai da ma’aikatan Najeriya ke fuskanta, maimakon ƙara musu nauyin kuɗaɗe.